• Buɗe burawuza.
 • Rubuta https://web.facebook.com/ a gurbin adireshi ko latsa nan. Shafi na ƙasa zai bayyana:
Hoto na 1: Shafin Fesbuk
 • Cike dukkan guraben da aka buƙata.
  • First name: Sunanka.
  • Surname: Sunan Mahaifi.
  • Mobile number or email address: Lambar waya ko adireshin Imel.
  • Password: Mabuɗi (Haɗaka ce ta harrufa da lambobi da suke a matsayin mabuɗin shafi. Ana matuƙar son sun zama na sirri sosai).
  • Birthday: Ranar Haihuwa (Ta haɗa da ranar haihuwa, watan haihuwa da kuma shekara. Misali: 2/2/2020).
  • Gender: Jinsi (Female – Mace. Male – Namiji).
 • Latsa Sign Up. Shafi na ƙasa zai bayyana: Create 2. Sannan kuma za tura maka lambobin tantancewa a matsayin gajeren saƙo.
 • Buɗe saƙonni ka ɗauko lambobin ka rubuta su a gurbin da ya dace.
Hoto na 2: Gurbin rubuta alƙaluman tantancewa
 • Latsa Continue. Allon sanarwa zai bayyana yana mai tabbatar maka da samuwar akwatunka.
 • Latsa Ok. Shafi na ƙasa zai bayyana.
Hoto Na 3: Matakin saka hoto
 • Latsa madannin Add Picture. Za ka ga wannan ya fito ko makamancinsa.

Hoto Na 4: ɗauko hoto

 • Zaɓi gurbin da ka adana hoto.
 • Yi tagwan latsa a kan hoton.
Hoto na 5: Asusun Fesbuk

Masha Allah. Yanzu ka gina shafin Fesbuk wanda kuma shi ne akwatunka na Fesbuk (Facebook Account). Wato asusunka na Fesbuk da za ka riƙa amfani da shi wajen hulɗa da abokai.

By admin

One thought on “Gina Shafin Fesbuk”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *