Yadda Ake Tarawa a Eksel (Kwamfuta)

Mai karatu, a wannan darasin za ka koya tare kuma da fahimtar yadda ake lissafin da ya shafi tarawa a Makirosoft Eksel a Kwamfuta. Ga matakan da za a bi daki-daki:

Akwai hanyoyi da dama da za a iya bi wajen tara lambobi a Makirosoft Eksel. A wannan darasin za mu taƙaitu da hanyoyi huɗu kawai. Ga su kamar haka:
1. Latsa kan akwatu na farko (A1).
2. Rubuta 20 a ciki.
3. Danna Enter daga jikin kibod.
4. Rubuta 30.
5. Danna Enter.
6. Rubuta 50.
7. Danna Enter.
8. Ɗan tsahirta ka latsa kan kowane akwatu da ka yi rubutu a ciki, sannan ka kalli akwatin suna, za ka ga sunan kowane akwatu a ciki.
9. Latsa akwatun farko, A1 da ka rubuta 20 a cikin.
10. Danna ƙulalin Shift daga jikin kibod.
11. Danna ƙulalin kibiya mai kallon ƙasa

An samo hoto daga shafin free icons
har zuwa kan akwatuna uku da ka yi rubutu a ciki (A1, A2 da A3). Za ka samu wannan hoton

12. Latsa kan wannan hoton.

Yana nan a saman shafin daga varin dama kusan qarshe-qarshe. Amsarka za ta zama 100.

Haka ne? Ka yi daidai.

Ko kuma
1. Bi mataki na ɗaya zuwa na 7 na sama.
2. Rubuta =A1+A2+A3, a cikin akwatun A4.

3. Danna Enter. Yaya, amsar ɗaya ce? Yawwa, amma fa kana da ƙoƙari!
4. Latsa nan ka juyi asalin aikin domin buɗewa a kwamfutarka.
5. Latsa akwatin A4.
6. Kalli akwatin fomula. Za ka ga yadda fomula take a ciki.

Ko kuma
1. Bi mataki na ɗaya zuwa na 7.
2. Rubuta =sum(A1:A3).

3. Danna Enter. Ka samu amsar? Haka na ke so.
7. Latsa nan ka juyi asalin aikin domin buɗewa a kwamfutarka.
8. Latsa akwatin A4.
9. Kalli akwatin fomula. Za ka ga yadda fomula take a ciki.

Ko kuma
1. Latsa akwatu na A2.
2. Rubuta 30.
3. Latsa akwatu na B5.
4. Rubuta 20.
5. Latsa akwatu na A10.
6. Rubuta 50.
7. Danna Enter.
8. Rubuta =sum(A2,B5,A10).

9. Danna Enter. Yaya, amsar ɗaya ce ko? Tafawa kanka da kanka.
10. Latsa nan ka juyi asalin aikin domin buɗewa a kwamfutarka.
11. Latsa akwatin A11.
12. Kalli akwatin fomula. Za ka ga yadda fomula take a ciki.