Kayan Aiki Eksel

Mai karatu, a wannan shafin zan xan yi maka bayani wasu kayayyakin aiki da kuma gaya maka ma’anar wasu kalmomi da suka shafi Eksel. Duka xaya ne a kwamfuta da waya. Ga su kamar haka:

1. Akwatin Suna Name Box: Gurbi ne da ke bayyanar da sunan akwatun da ka ke aiki a ciki.

Hoton Akwatin suna
2. Akwatun Fomula Formula Bar: Gurbi ne da ke bayyanar da duk abin da ka rubuta a cikin akwatin da ka ke aiki a cikinsa.

Hoton Akwatin fomula
3. Akwatu Cell: A cikinsa ake rubuta duk abin da ake rubutawa. Kowane ɗaya yana da suna guda ɗaya rak, da ya keɓanta da shi. Misali A1 shi kaɗai ne.

Hoton Akwatin rubutu
4. Row: Shi ne jerin gidan dara da ya fara daga hagu zuwa dama. Kowane row yana da wakilci na lamba, wanda yawansa ya kai miliyan ɗaya da dubu arba’in da takwas da ɗari bakwai da hamsin da shida (1,048,756). Yana farawa daga 1 zuwa 1048576.


5. Kolum Column: Shi ne jerin akwatuna daga sama zuwa ƙasa. Yana da wakilcin harrufan ABCD.

Hotunan Kolum da ke nuna na farko da na qarshe
6. Madannin Shafi Sheet Tab: Shi ke buɗe maka shafi idan ka danna.

Hoton Madannin Shafi (Sheet tab)

Ma’anar Kalmomi
1. Worksheet: Shi ne shafin Makirosoft Eksel da ka ke aiki a ciki.
2. Workbook: Haɗakar shafuka biyu ko fiye da haka. Idan ka buɗe Eksel nan take kana da littafi mai shafuka 3 (Sheet1, Sheet2 da Sheet3) a Eksel 2010 zuwa ƙasa.
3. Adireshin akwatu Cell Reference: Shi ne manunin kowane akwatu; wanda ke bambanta ɗaiɗaikun akwatuna daga saura. Yakan samu daga haɗakar harafin kolum da kuma lambar ro. Misali A1 yana nufin akwatu mai lamba ɗaya na layin A.
4. Fomula Formula: Ita ce abar da ke ƙulla dangantaka tsakanin dukkan akwatunan da ke cikin Eksel sannan kuma ta ke jagorantar kowane irin lissafi.
5. Alamomin Lissafi Operators: Su ne duk wata alama ta lissafi, kamar irin su + x da sauransu

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *