Tarawa (Waya)

Tarawa
Akwai hanyoyi uku da ake amfani da su wajen tara lambobi a Eksel:
1. Ta hanyar amfani da fonkshin waɗanda suma guda biyu ne kamar haka:
(i) =sum(A3:A30). Wannan fomula za ta tara maka dukkan lambobin da ke cikin gidaje tun daga A3 har zuwa A30 a jere. Wannan alama (:) tana nufin daga A3 zuwa A30.
1. Shiga shafin Eksel.
2. Dangwali gidan dara A1. Za ka ga zaɓuka sun fito.


3. Dangwali Edit. Za ka ga Kibod yafito.


4. Rubuta SN.
5. Danna Tab daga jikin Kibod yana nan a gefen dama na gurbin da ka yi rubutu a jikin Kibod. Za ka ga rubutun ya shiga gidan dara na A1, sannan kuma A2 ya zama cikin shiri.


6. Rubuta KAYA.
7. Dangwali Tab.
8. Rubuta FARASHI.
9. Dangwali Enter daga jikin Kibod.
10. Rubuta 1.
11. Dangwali Tab
12. Rubuta Littafi.
13. Dangwali Tab.
14. Rubuta 1250
15. Dangwali Enter.
16. Rubuta 2.
17. Dangwali Tab.
18. Rubuta Biro.
19. Dangwali Tab.
20. Rubuta 256.
21. Dangwali Enter.
22. Rubuta 3.
23. Dangwali Tab.
24. Rubuta Pencil.
25. Dangwali Tab.
26. Rubuta 700.
27. Dangwali Enter.
28. Rubuta 4.
29. Dangwali Tab.
30. Rubuta Paper.
31. Dangwali Tab.
33. Rubuta 215.
34. Dangwali Enter.
35. Rubuta 5.
36. Dangwali Tab.
37. Rubuta Erasor.
38. Dangwali Tab.
39. Rubuta 600.
40. Dangwali gida mai lamba C7.
41. Rubuta =sum(C1:C6).


42. Dangwali Enter. Eksel za ta tara maka jimillar kuxaxen da ke cikin gidajen da ke sama da wanda ka rubuta fomula daga na farko zuwa na ƙarshe.

Dangwali nan ka juyi asalin aikin a Eksel