Fitar da Sakamakon Jarabawa (Waya)

Ɗaya daga cikin manya-manya kuma muhimman amfanin na’urorin laturonik shi ne sauƙaƙa wa jama’a yadda suke gudanar da harkokin yau-da-kullum. Gudanar da lissafi mai sarƙaƙiya cikin sauƙi, sauri tare kuma da ƙaranta kurakurai na daga cikin irin wahalhalun da suka zama sauƙaƙan lamura. A wannan darasin, zan yi ƙoƙarin sada ku da turba mafi sauƙi ta gudanar da lissafin fitar da darajar makin jarabawa da ɗalibi ya samu ta hanyar amfani da wayar hannu. Ga yadda abin yake:
1. Buɗe Makirosft Eksel.
.

2. Dangwali Kibod.


3. Dangwali Akwatin A1.
4. Rubuta SN.


5. Dangwali Tab.

6. Rubuta Name.
7. Dangwali Tab.
8. Rubuta Gender.
9. Dangwali tab.
10. Rubuta Assignment 10%.
11. Dangwali tab.
12. Rubuta Test1 10%.
13. Dangwali tab.
14. Rubuta Test2 10%.
15. Dangwali tab.
16. Rubuta CA 30%.
17. Dangwali tab.
18. Rubuta Exam 70%.
19. Dangwali tab.
20. Rubuta Total.
21. Dangwali tab.
22. Rubuta Grade.
23. Dangwali Enter.

24. Rubuta 1.
25. Dangwali tab.
26. Rubuta Ado Bala.
27. Dangwali tab.
28. Rubuta Male.
29. Dangwali tab.
30. Rubuta 6.
31. Danwgali tab.
32. Rubuta 8.
33. Dangwali tab.
34. Rubuta 5.
35. Dangwali tab.
36. Sake dangwalar tab. Za ka bar akwatin CA (G2) babu komai a ciki.
37. Rubuta 45.
38. Dangwali tab.
39. Sake Dangwalar tab.
40. Dangwali Enter.


41. Yi ta maimaita matakai na 24 zuwa na 40 har sai ka rubuta sunayen ɗalibai 10.


42. Dangwali G2.
43. Rubuta =sum(d2:f2).

44. Dangwali Enter. Za ka ga Eksel ta rubuta maka 19 a cikin akwatun G2.

45. Sake dangwalar G2.
46. Dangwali kusurwar dama taƙasan akwatin G2.

47. Dangwali Fill.


48. Dangwali kibiya mai kallom dama ka ja ƙasa zuwa gida na ƙarshe (G11). Kana ɗage hannunka za ka ga Eksel ta lissafa maka sauran.


49. Dangwali akwatin I2.
50. Rubuta =sum(G2,H2).

51. Dangwali Enter.

53. Sake dangwalar I2.
54. Dangwali Kusurwar dama ta ƙasa.
55. Dangwali Fill.
56. Dangwali kibiya mai kallon ƙasa ka tura zuwa gida na ƙarshe.


57. Dangwali J2.
58. Rubuta =if(i2>=80,”A”,if(i2>=70,”B”,if(i2>=60,”C”,if(i2>=50,”D”,if(i2>=40,”E”,if(i2<40,”F”)))))).


59. Dangwali Enter.


60. Sake dangwalar J2.
61. Dangwali kusurwar ƙarshe ta ƙasa.
62. Dangwali Fill.
63. Dangwali kibiya mai kallon ƙasa ka ja zuwa akwati na ƙarshe ta ƙasa.


Daga ƙarshe wannan shi ne sakamakon.


Madalla da wannan fasaha. Na tabbata, duk malamin makarnatar da ya ci karo da wannan zai ce sauƙi ya zo. To, kar ka yi rowa, daure ka turawa saura suma su amfana. Alal aƙalla koda mutum guda ne.
Dangwali nan ka juyi asalin aikin.